This is an old revision of the document!
Ita kadai ce matashiyar jaruma cikin wannan jerin shahararrun 'Jarumai 10 Da Suka Taka Rawar Gani A 2016.' Fim din Tabbataccen Al'Amari shi ne wanda ya sanya wannan jaruma darewa matsayi na tara cikin jerin, domin ta shiga tsakiyar gogaggu ta nuna gogewarta.
Kasancewar labarin fim din kusan a kanta yake, hakan ya bata damar taka rawarta har da tsalle. Domin mafiya yawan wadanda suka kalli shirin maganar ta kawai suke yi ba ta sauran jaruman ba.
* Dan Saurayi((1st film)
Published by AREWA24's Kundin Kannywood on Jan 7, 2016
Yan mata samari na fuskantar kalu bale da yawa daga ciki da wajen masana'antar fina-finai a kokarin su na tabbatar da burin su da kuma mafarkin rayuwa. Shirin ya tattauna da jaruma a kokarinta na neman yanci, gindin zama da kuma dogaro da kai.